Bayan Auren Wasu Jarumai A Kannywood Wasu Maganganu Sun Biyo Baya

Bayan Auren Wasu Jarumai A Kannywood Wasu Maganganu Sun Biyo Baya
Bayan Auren Wasu Jarumai A Kannywood Wasu Maganganu Sun Biyo Baya

Bayan da akayi auren wasu jarumai fitattu a cikin jaruman Kannywood an yi ka-ce-na-ce. Maganganun basu yi ma wasu daɗi ba wasu kuma suka yi ko oho da al’amarin.

Bayan Auren Wasu Jaruman Kannywood Wasu Kananan Maganganu Sun Biyo Baya

A lokacin jaruma Hafsat Idris ta yi aure mutane da yawa sun yi zargin ta auri wani daga cikin Ƴaƴan tsohon shugaban kasar Nigeria ne kamar yadda aka sansu suna soyayya tun talitali. Sai dai kuma jarumar ta fito ta yi bayani wa jama’a ta ce, “Ba Ɗan Sani Abacha ne na aura ba, kamar yadda kuka yi tsammani. Shi aure nufi ne na Ubangiji shi kadai ya isa ya tabbatar da wanda kowanen bawansa zai aura. Ba ɗan Sani Abacha kaɗai ne ya zo neman aurena ba, don haka kada kuce na yaudare shi ne, A’a haka Allah ya nufa ba shi ne mijin da zan aura ba.

Haka lokacin da akayi auren Jaruma A’isha Aliyu Tsamiya. Ba tare da wani sanarwa ba mutane sai ganin sukayi an ɗaura aurenta da wani daga cikinmasoyanta. Mutane da yawa sun yi maganganu. Wasu cewa suke saboda bata bukatar ganin kowa a wurin bikin nata ne yasa bata gayyaci kowa ba, wasu kuma suka ce tsabar rowa ne kawai yasa ba ta gayyaci kowa ba. To amma dai ita cewa ta yi, “An yi aurena ne ba tare da sanin jama’a ba saboda bana son wahalar da kowa kamar yadda lokaci ya sauya kudin mota yayi tsada saboda tsadar mai da Nigeria take ciki.”

Sai kuma auren Hassana Muhammad tare da jarumi kuma Furodusa Bashir Mai Shadda. Jaruma Hassana Muhammad ta samu kalubale na kiraye-kiraye da ta samu a wurin jama’a. Mutane da yawa sun kirata suna faɗa mata da cewa Bashir Mai Shadda Azzalumi ne saboda sun ga ya yi niyyar auren A’isha jarumar da ake shirin A Duniya da ita.

Jarumar Hassana Muhammad ta ce, “Ba kamar yadda jama’a suka dauka ba ne, babu wata alaƙa kowace iri idan ka cire ta masana’antarmu Kannywood. Hotuna da videos da akayi tsakanin Bashir Maishadda da A’isha duka wannan shiri ne wani talla ne suke tsaraba inda aka zabe su a matsayin mata da miji. Amma banda wannan babu wani abu a tsakaninsu haka nan kuma Bashir Maishadda mutumin kirki ne wannan ne yasa nake sonsa rokona a wurinku dai ku tayani addu’a Allah ya sa mu samu albarka dake cikin rayuwar auremmu.”

Jaruma Fati Washa kuma ta yi wani posting a shafin ta na Instagram wanda yayi kama da tana dab da amarcewa.

About Hausabeats 1317 Articles
Mustafa Yakubu is a Nigerian music and entertainment writer covering trending celebrity news, viral stories, and latest song releases. He focuses on African pop culture and breaking entertainment updates.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*