Kalaman Masoya Domin Valentine Wato Ranar Masoya

Kalaman Masoya Domin Valentine Wato Ranar Masoya
Kalaman Masoya Domin Valentine Wato Ranar Masoya

Yau ne Ranar Masoya Ta Duniya Ga Kyakkyawar Wasika Mai Dauke Da Addu’a Zuwa Ga Masoyiya.

Ina alfahari da wannan ranar ba don kasancewarta ranar valentine ba sai don yadda masoya ke farin ciki a cikinta. Idan na ce miki yau ne ranar mu kenan ma akwai ranar da ba tamu ba kuma fadin hakan kamar algus ne domin kodayaushe kina raina, dake nake bacci dake tashi.

Ina Son Ki ita ce kalmar da nake ji kamar na bude kunnenki na furta sosai, amma yadda nasanki da nutsuwa nasan ba sai na yi ihu ba kin fahimta. Ina Son Ki, ina ƙara Son Ki.

Assalamu Alaikum kyakkyawar duniya daya wacce ta kere dubu. Hakika ke tamkar farin wata mai kwana sha hudu ce. Ahalina suna min barkan samun macce ta gari, mai cikakkiyar kamala da nutsuwa. Masoyiyata idan na ganki mantawa nake da wata kalma mai suna damuwa. Ina sonki irin son da bana yiwa kowa, domin soyayyar kice ke karamin himma a dukan al’amurana.

Addu’a Zuwa Ga Masoyi

Assalamu Alaikum ya Nurrul khairan zuciyata hasken farin wata mai yaye dukan damuwata, ruwan zam-zam mai wanke dukan dattin zuciyata. Ina roka maka Allah ya kare ka daga dukan masu sheri. Ina roka maka Allah yayi maka dukan damuwarka ya haskaka a cikin masu haske ya baka Sa’a a cikin kowane al’amarin rayuwarka.

About Hausabeats 1325 Articles
Mustafa Yakubu is a Nigerian music and entertainment writer covering trending celebrity news, viral stories, and latest song releases. He focuses on African pop culture and breaking entertainment updates.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*