Zafafan kalaman soyayya da ke jefa mata a tarkon kauna Hakika ke kyakkyawa ce, tamkar zinariya ga iya takun kasaita tamkar jimina, kwalliyarki na rikita mai kallonki
Kalaman sanyaya zuciya, yabon masoyi, kogin soyayya, yadda zaka sace zuciyar budurwa, ko da kauna, masoya, rayuwar masoya,
Zafafan kalaman soyayya da ke jefa mata a tarkon kauna
Hakika ke kyakkyawa ce, tamkar zinariya ga iya takun kasaita tamkar jimina, kwalliyarki na rikita mai kallonki, surar jikinki na sanya maza tuntube har su fadi basu sani ba.
Hakika ke yar gidan manya ce yar gida mai asali da kuma tarbiyya, hakika ke yar babban gida ce kin fito daga gidan mutunci sannan kuma karamci da kawaici da tausayi da kuma kyautatawa dukkan su halaye na da suka fito daga gidanku.
Tabbas duk wanda ya sameki a matsayin matar aure ya gama samun komai a duniya, sai dai kawai ya jira lahirarsa ta yi kyau.
Na yi alkawarin maishe da ke tamkar sarauniya a cikin gida na mudfdin ki ka aureni, sannan kuma na yi alkawarin tanadar miki da dukkan farincki a cikin gidana ta yadda za ki manta da wata kalma da ake kira damuwa.
Kedai kawai ki bani dama ta hanyar mallaka nimi zuciyarki, ma’ana ki bani soyayyarki ni kuma zan baki kulawar da duk duniya ba namijin da zai iya baki kamar ta.

Leave a Reply