Zafafan Kalaman Soyayya 2027

Zafafan Kalaman Soyayya 2027

Kamar yadda muka saba kawo muku sabbin zafafan kalaman soyayya a kowace shekara, yau ma mun kawo muku sabbin zafafan kalaman soyayya 2023.

A wannan karon mun kawo kalaman soyayya masu dadi, da kalaman soyayya na zamani, da kuma kalaman soyayya masu kara dankon kauna.

Gasu kamar haka:

Hakika so wani linzami ne da ke jan dukkan gangar jiki zuwa inda ya so, ki sani ya ke sarauniyar mata so da kaunarki sun mamaye dukkan illahirin sassan jikina ya zama linzami, ina rokonki da ki jani a hankali har zuwa fadar zuciyarki domin ki nada ni sarki a fadarki.

Ya ke haske da ke haskaka dukkan rayuwata, ya ke fitila da ke yaye dukkan dubu a gareni, ki kasance sanyi domin domin kawar da dukkan wani sauyin yanayi da ka iya shigowa rayuwata.

Ni kuma zan zame miki garkuwa da ke bada kariya ga dukkan wani kalu bale da ka iya tunkaro rayuwarki.

Kammalawa

A nan za mu ga cewa anyi amfani da hikima ta jibantuwa a cikin wannan kalaman soyayya masu jan hankali.

Domin kalaman soyayya daga kundin masoya shi ne abu mafi kyau da zai dora ka a bisa mizanin cin nasara a soyayya

About Hausabeats 1325 Articles
Mustafa Yakubu is a Nigerian music and entertainment writer covering trending celebrity news, viral stories, and latest song releases. He focuses on African pop culture and breaking entertainment updates.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*